Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia)
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.

An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Mujallar Mustabsirin
Sep 15 2024
Tunawa da Shahadar Annabi Muhammad (s)
Shahadar Imam Muhammad Baqir (a.s)
Shi Imam Muhammad Baƙir (a.s) ya fita daban a cikin A’imma (a.s), ta yanda ya zamo shi ta ko ina a nasaba shi:
Muhammady ne kuma Alawi ne sannan Fatimi. Don kuwa Imam Ali ɗan Husain ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib (a.s) ne ya haife shi.
Mahaifiyarsa kuwa ita ce Fatima ‘yar Imam Hasan Almujtaba ɗan Ali ɗan Abu Ɗalib (a.s)…
Haka nan shi da ɗansa Imam Ja’afar Assadiƙ (a.s) sun fi duk sauran A’imma samun damar karantar da al’umma koyarwar gidansu, shi ya sa a duniyar Shi’a da Sunna za ku ga Hadisansu sun fi yawa a bisa sauran A’imma (a.s).
Sep 15 2024
BAYAN KISAN KARBALA RANAR ARBAIN
AYARIN SHAHIDAI A KUFA
MAI RUWAYA: Muslim Jassas yana cewa:
MUSLIM JASSAS: Ni na gani da idona a lokacin da aka shigo da ayarin fursunonin yaki cikin Kufa, mutane suna ba yaran da ke fama da tsananin yunwa gurasa da dabino, sai Ummu Kulsum ta daka masu tsawa tana mai cewa:
UMMU KULSUM: Ya ku mutane! Bai wa zuriyarmu sadaka haramun ne.
MAI RUWAYA: Sai aka amshe gurasa da dabinon da ke hannun yaran aka mayar masu da kayansu, su kuma mutanen suna ta rusa kuka.
Ibn A’asam Al-Kufi ya rubuta cewa: A lokacin da Umar ibn Sa’ad yake tahowa da ayarin Ahalil Baiti a matsayin fursunonin yaki zuwa Kufa, sai Ibn Ziyad ya ba da umarnin a tsittsire kawukan shahidai a kan masuna a saka su a gaban kamammun yakin a ci gaba da tafiya a haka, kai na farko wanda aka fara tsirewa sama shi ne kan Imam Husain (as)!
A lokacin da ayarin ya isa Kufa, sai mutane suka dinga kururuwa suna koke-koke, nan take sayyida Zainab (as) ta daka masu tsawa ku rufe mana baki! Bayan nan ta yi godiya ga Allah ta yi salati ga Annabi, sannan ta fara magana tana mai cewa:
SAYYIDA ZAINAB: Ya ku mutanen Kufa! Ya ku mayaudara, marasa cika alkawari, ya ku makirai! Har abada kada Allah ya sa hawayenku su bushe, kada Allah ya sa kururuwarku ta lafa!
ZURIYAR SHAHIDAI A FADAR IBN ZIYAD
MAI RUWAYA: Fursunonin Karbala an dunguma da su fadar Ibn Ziyad da ke Kufa. Ibn Ziyad da kalmomi masu daci da bacin rai ya fara, nan da nan tattaunawa ta shiga tsakanin Ibn Ziyad da sayyida Zainab (as).
IBN ZIYAD: Godiya ga Allah wanda ya wulakanta ku ya kashe ku, kuma ya nuna cewa duk abin da kuke fada karya ce tsagwaronta!!
SAYYIDA ZAINAB: Godiya ta tabbata ga Allah wanda ya girmama mu ta hanyar Manzonsa ya kuma tsarkake mu daga dukkan kazanta. In ba fasiki ba babu mai wulakanta, kuma in ba mai mummunan aiki ba babu mai shirga karya, kuma mu ba masu mummunan aiki ba ne sai dai wasunsunmu.
IBN ZIYAD: Duba ki ga abin da Allah ya wulakanta ahalinki da shi?
SAYYIDA ZAINAB: Ni ban ga komai ba sai kyakkyawa – wadannan wasu mutane ne da Allah ya kaddara cewa kashe su za a yi, su kuma sun sallamawa hukuncin Allah suka tafi makwancinsu na har abada.
IBN ZIYAD: Allah ya ye mani ciwon da ke cikin zuciyata da kashe dan uwanki Husaini marar biyayya, iyalansa da rundunarsa!
SAYYIDA ZAINAB: Na rantse da Allah haka ne kun kashe mani shugaba, kuma kun yi nufin ganin bayan tsatsona kun nemi ku tunbuke mani asali, idan wannan danyen aikin sababi ne na warakarka to lallai haka ne ka samu lafiya!
***
KUFA – CI GABAN TATTAUNAWAR IBN ZIYAD DA SAYYIDA ZAINAB
MAI RUWAYA: Sai Ibn Ziyad ya juyo ya kalli Imam Sajjad sannan ya tambaya:
IBN ZIYAD: Wane ne wannan?
WASU DAGA MABIYAN IBN ZIYAD: Wannan Aliyu ibn Husain ne.
IBN ZIYAD: Shin daman Allah bai kashe Aliyu ibn Husain ba?
IMAM SAJJAD: Ina da dan uwa shi ma sunansa Aliyu ne, Aliyu Akbar, mutane sun kashe shi!
MAI RUWAYA: Sai Ibn Ziyad ya lura cikin izza da gwarzontaka yake ba shi amsa, sai ya fusata sannan ya ba da umarnin cewa a sare masa kai! A daidai wannan lokacin ne goggonsa sayyida Zainab ta yi wuf ta rungumo shi jikinta, sannan ta ce:
SAYYIDA ZAINAB: Ya kai Ibn Ziyad! Jinananmu da kuka zubar sun isa haka! Ina rantsuwa da Allah wannan kam ba zan bayar da shi ba, amma idan ka matsa to mu duka biyun ka kashe mu!
IMAM SAJJAD: Shin da mutuwa kake mana barazana? Shin ba ka san cewa dama can mu an saba kashe mu ba, kuma shahada abin alfaharinmu ce ba?!
MAI RUWAYA: Nan take sai Ibn Ziyad ya janye umarninsa, sannan ya ce:
IBN ZIYAD: Ai ina ma tsammanin wannan rashin lafiyar ma ita da kanta za ta karasa kashe shi!
BACIN RAN ZAID IBN ARKAM
MAI RUWAYA: An nakalto cewa: Ibn Ziyad ya ajiye kan Imam Husain (as) a gabansa sannan ya dinga sanya wata sanda da yake rike da ita a hannunsa yana tattaba idanu, hanci da labban Imam yana fadin:
IBN ZIYAD: Kai wadannan hakora akwai kyau!
MAI RUWAYA: Ana cikin wannan hali ne Zaid ibn Arkam, daya daga cikin sahabban Manzo mai girma, ya fashe da kuka sannan ya daka wa Ibn Ziyad tsawa yana mai fadin:
ZAID IBN ARKAM: Kai Ibn Ziyad cire wannan sandar taka daga nan, domin ina rantsuwa da Allah ni din nan na sha gani da idanuna Manzon Allah (s.a.w.a) yana sanya labbansa masu albarka a bakin Imam Husain (as) kuma yana sumbatarsa.
IBN ZIYAD: Amma lallai ba domin tsufa ya kama ka hankalinka ya fara gushewa ba da na sare maka wuyanka!
MAI RUWAYA: Zaid ibn Arkam cikin fushi ya tashi ya fice daga fadar.
KULLE AYARIN KUMAJIN KARBALA CIKIN KURKUKU
MAI RUWAYA: Ibn Ziyad sai ya ba da umarnin cewa a kulle ayarin shahidan Karbala cikin kurkukur Kufa. Sannan ya aika da wasika zuwa ga Yazidu a can Sham yana mai sanar da shi halin da ake ciki.
Bayan nan sai ga sako daga Sham zuwa ga Ibn Ziyad ana ba shi umarnin ya aika fursunonin yaki tare da kan Imam Husain (as) da kawukan sauran shahidai zuwa Sham.
***
DAGA KUFA ZUWA SHAM
MAI RUWAYA: An tasa keyar ayarin shahidan Karbala daga Kufa zuwa Sham a ranar 19 ga Muharram shekara ta 61 bayan hijira suka isa a ranar 1 ga Safar shekara ta 61, saboda haka a bisa wannan lissafin ayarin Karbala sun isa birnin Sham a cikin kwana 12 kenan.
Kamar yadda ya zo a tarihi shi ne cewa shi kan Imam Husain (as) da kawukan sauran shahidai tun kafin a kama hanya da ayari, aka aika da su zuwa Sham, amma a kan hanya sai suka hadu da juna sannan aka shigar da su tare zuwa cikin gari!
Yazidu ya yaudari jama’a ta hanyar yada karairayi, ta yadda ya nuna wa jama’a cewa wadannan wadansu fursunonin yaki ne wadanda suka yi wa kalifan musulmi tawaye to sai a wajen yaki aka kashe mazajensu su kuma wadannan kawukan da kuke gani to kawukan wadanda aka karkashe masu din ne.
HUDUBAR SAYYIDA ZAINAB
MAI RUWAYA: Ayarin fursunonin Karbala sun isa Sham…. Sayyida Zainab (as) a lokacin da ta lura jama’ar da ke cikin wannan fadar za su iya sauraren jawabanta, sai ta raya a ranta cewa to lallai bai kamata in yi shiru game da wannan babban zaluncin ba, don haka sai kawai ta mike tsaye ta fara huduba. A cikin hudubarta ta bayyana aibin zalunci da rashin adalci, tana mai fadin cewa:
SAYYIDA ZAINAB: Har abada ba za ka taba kubutar da kanka daga wannan bata sunan da kai wa kanka ta hanyar zaluncinka (daga zukatan mutane) ba…. Ka sani kwanakinka a mulkin ‘yan kadan ne, jama’arka za su tarwatse daga gare ka, har zuwa ranar da mai kira zai yi yekuwa cewa: to la’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai!
MAI RUWAYA: Haka nan ma ta yi bayani game da matsayi, daukaka da gaskiyar da ke tare da Ahlul Bait (as) ta kuma kara yin godiya ga Allah cewa ya kara daukaka su, su Ahlul Bait da shahada wanda a karshen jawabin nata ta karkare da karanto bangaren karshe na aya ta 18 a cikin suratul Hud kamar haka:
SAYYIDA ZAINAB: Ku saurara! La’anar Allah ta tabbata a kan azzalumai!
SHAWARAR YAZIDU DA MUTANEN SHAM
MAI RUWAYA: Bayan zazzafar hudubar da sayyida Zainab (as) ta gabatar wacce ta yi wani irin tasiri a wannan fada ta Yazidu. To sai Yazidu ya juyo ya gurin mutanen Sham wadanda suke zaune a cikin fadar sannan ya ce:
YAZIDU: Mai za ku ce game da wadannan fursunonin? Shin kuna ganin in kashe su ne?
MAI RUWAYA: Sai Nu’uman ibn Bashir ya ce:
NU’UMAN IBN BASHIR: Ka yi nazari ka gani, yanzu da a ce Manzon Allah yana gurin nan mai zai yi, to kai ma ka yi kamar hakan!
MAI RUWAYA: Kowa ya ba da shawarasa da ra’ayinsa kan yaya ya kamata a yi da su. wasu kuma sai kuka suke yi suna fadin:
MURYOYIN MUTANE: In ba mutane marasa tsarki ba, babu wanda zai kashe ‘ya’yan Manzon Allah (s.a.w.a)!
MAI RUWAYA: Yazidu sai ya lura idan aka ci gaba da wannan zaman to ba zai masa kyau ba, nan da nan sai ya ba da umarni a tafi da wadannan fursunonin yakin wani gida da yake kusa da fadarsa kafin yayi tunanin mai ya kamata ya yi masu.
***
HUDUBAR IMAM SAJJAD (AS) A SHAM
MAI RUWAYA: Limamin Juma’a ya yi huduba a nan cikin fadara Yazidu, kuma a cikin hudubar tasa duk abin da ya zo bakinsa na aibatawa dangane da Ahlul Bait da ayarin kamammun fursunonin Karbala ya fade shi, kuma ya yi ta kokari wajen yabo da kambama Yazidu iyakar iyawarsa!
Amma Imam Sajjad (as) sai ya cewa Yazidu:
IMAM SAJJAD: Ko za ka ba da dama ni ma na yi magana, maganar da a cikin akwai yardar Allah!
MAI RUWAYA: Da farko Yazidu yaki ya ba da wannan damar. Amma dansa sai ya matsa masa a kan sai ya bayar da wannan damar ga Imam.
IMAM SAJJAD: Ya ku jama’a ku sani! Allah Ta’ala ya ba mu wadansu halaye guda shida (mu Ahlul Bait (as)), ya kuma daukaka mu da wasu kebantattun abubuwa guda bakwai, ya ba mu: Ilimi, juriya, yafiya, fasaha, gwarzontaka da kuma soyayya a zukatan muminai; sannan kuma sai ya kebance mu da wata daukaka cewa mu ne muke da: Mazon Musulunci, Siddik (mai gaskiya abin gaskatawa), Ja’afar Dayyar, Zakin Allah kuma Zakin Manzon Allah (s.a.w.a) wato (sayyiduna Hamza) da kuma jikokin Manzo Hasan da Husain (as).
Wanda ya sanni to hakika ya sanni, wanda kuma bai sanni ba to zan ba shi labarin asalina da tsatsona.
Ya ku mutane ku sani! Ni dan Makka da Mina ne, ni dan Zam-zam da Safa ne, ni dan wanda ya sa hannunsa mai albarka ne ya dauki Hajarul Aswad ya dora shi a mazauninisa, ni dan wanda yake shi ne mafi daukakar mahajjata da masu yin Talbiyya ne, ni dan wanda ya hau Buraka ne, ni dan wannan Manzon nan ne wanda a dare guda ya yi isra’i daga masallacin Harami zuwa masallacin Aksa (Quds) ne, ni dan wannan ne wanda mala’ikun sama suka yi sahu a bayansa ya ja su sallah, ni dan Manzon nan ne wanda Allah mai girma da daukaka ya aiko masa da wahayi, ni dan Muhammad Mustafa ne.
Ni dan Ali Al-Murtadha ne, dan wanda yake bai wa Haramin musulmi kariya ne…..
Kuma shi ne wannan wanda ya kasance mai gwarzontaka, mai yawan yafiya da kauda kai, mai yawan fara’a, mai yawan alheri, madaukaki, mai kawo dauki a yayin da aka shiga matsaloli, mai yawan hakuri, mai yawan azumi, tsarkakakke daga dukkan aibobi kuma mai yawan sallah.
Ni dan Fatima Al-Zahra’u ne, ni dan shugabar matan talikai ne….. Haka ya ci gaba da jawabi cikin izza da daukaka, har mutanen wurin gabaki daya suka rude da koke-koke!
***
Jul 7 2024
Watan Muharram Da Abubuwan Da Ya Kunsa

Watan Muharram wata ne mai alfarma, wata ne da yake daya daga cikin watannin da ake kiran su da Ashhurul Hurum, wato Watanni Madaukaka; wadanda aka haramta yin yaki a cikinsu. Wata ne na farko a kidayar watannin Kamariyya guda goama sha biyu a Musulunci.
Jul 7 2024
Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci 1446h

Shigowar Sabuwar Shekarar Musulunci: Kamar yadda muka sani a duk ranar daya ga watan Muharram, rana ce da ake lissafinta a matsayin ranar shigowar sabuwar shekarar Musulunci a wajen dukkan Musulmi wato shekarar Hijiriyya Kamariyya, kuma daga nan ne ake fara lissafin wata-wata na watannin Musulunci kama tun daga shi watan na Muharram da Safar da Rabi’ul Awwal haka dai haka dai har zuwa watan goma sha biyu wato watan Zulhijja. To ita wannan rana, rana ce mai girma da kuma rana ce da a tarihi ya zo cewa….
Jul 2 2024
Ranar Mubahala
Ranar Da Manzon Allah (S) Ya Fito Yin Mubahala Da Kiristocin Najaran Tana Nufin:
Duk duniya Manzon Allah (saww) ba shi da tamkar waɗanda ya fito da su wato Imam Ali (a.s) da Sayyida Faɗima Azzahara (a.s) da ƴaƴanta Imam Hasan da Imam Husain (a.s) domin da yana da waɗanda suka fi su ko tamkarsu to da ya fito da su a wannan rana. More
Jun 27 2024
Murnar Haihuwar Imam Musa Kazim (a.s)
TAKAITACCEN TARIHIN IMAM MUSA AL-KAZIM (AS)
Nasabarsa: Imam Musa Al-Kazim (as), d’an Imam Ja’afar As-Sadiq (as), d’an Imam Muhammad Al-bakir (as), d’an Ali Zainul-Abidin (as), d’an Imam Husain Sayyidus-Shuhada (as); kanin Imam Hasan Al-Mujtaba (as), ‘ya’ya Ali bin Abi Talib (as) da Fatimah Az-Zahra (as); ‘yar Annabi Muhammad (saw). More
Jun 26 2024
ALLAH NE YA UMARCI ANNABI MUHAMMAD (S) YA NAƊA ƘANINSA IMAM ALI (AS)
ALLAH NE YA UMARCI ANNABI MUHAMMAD (S) YA NAƊA ƘANINSA IMAM ALI (AS) A MATSAYIN HALIFA NA FARKO A BAYANSA; DA NASSIN AYAR ISAR DA SAKO (AYAR TABLIGI):

Allah (swt) yana cewa:
“Ya kai Annabi (saw)! isar da abinda Allah ya aiko maka; idan ba ka isar ba tamkar ba ka isar da sako ba; tabbas! Allah zai kiyayeka daga mutane” (Q : 5 : 67):
يا ﺃﻳﻬﺎ ﺍﻟﺮﺳﻮﻝ ﺑﻠﻎ ﻣﺎ ﺃﻧﺰﻝ ﻣﻦ ﺭﺑﻚ ﻭﺇﻥ ﻟﻢ ﺗﻔﻌﻞ ﻓﻤﺎ ﺑﻠﻐﺖ رسالته
(Al-Ma’ida : 67).
Manyan malaman Ahlus-Sunnah a fagen Tafsiri da Hadisi da Asbabun-Nuzul… Sun tabbatar da cewa wannan ayar ta sauka ne daf da al’amarin Ghadir, kuma bayan Mala’ika Jibril (as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi (saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta masu cewa Imam Ali (a.s) ne halifa a bayansa:
Fakhrud-Deen Ar-Razi (Babban malamin Ahlus-sunnah) ya tabbatar da cewa; Ayar isar da sako (Ayatut-Tablig) ta sauka ne daf da al’amarin Ghadir, kuma bayan Mala’ika Jibril (as) ya sauko da wannan ayar ne Annabi(saw) ya tara Sahabbansa a Ghadir Khum ya shelanta cewa Imam Ali(as) ne maula (Shugaba / halifa) a bayansa:
Jun 22 2024
TAYA MURNAR HAIHUWAR IMAM ALIYU AL-HADI (AS)
HAIHUWAR IMAM ALIYU AL-HADI (AS)

TAKAITACCEN TARIHIN IMAM ALI AL-HADI(AS):
Nasabarsa ta bangaren mahaifinsa: Imam Ali Al-Hadi (as) ɗan Imam Muhammad Al-Jawad (as), ɗan Imam Ali Ar-Rida (as) ɗan Imam Musa Al-Kazim (as), ɗan Imam Ja’afar As-Sadiq (as) ɗan Imam Muhammad Al’baƙir (as) ɗan Ali Zainul-Abidin (as) ɗan Imam Husain Sayyidus-Shuhada (as) ƙanin Imam Hasan Al-Mujtaba (as) ‘ya’ya Ali bin Abi Talib (as) da Fatimah Az-Zahra (as); ‘yar Annabi Muhammad (S).
Mahaifiyarsa:
Jun 17 2024
Muna Maku barka da Salla – 10 Zulhijja Ranar Salla Babba
Sallar Idin Layya = Babbar Sallah
KA’ABA
*Takaitaccen Tarihin*
*Sayyid Sharif:*
*Shibuli Sharif Ibrahim*
Jun 17 2024
Shahadar Muslim ibn Akil
Shahadar Muslim ibn Akil
Innalillahi wa inna ilaihi raji’un
A ranar Arfa, Yazidu Ɗan Mu’awuya Jikan Abu Sufiyan da Hindu (Magatsiyar Hantar Syed Hamza) ya sa Hajjaj ya kashe Muslim Ɗan Akeelu, wanda Imam Hussaini(as) ya aike shi garin Ƙufa domin isar da saƙon taimaka masa wurin yaƙar zalunci.
Mukabalolin Mustabsirin
Jul 5 2024
DAGA MADINA ZUWA MADINA; AYARIN MASU KUMAJI – 3
FARAWAR QISSAR KARBALA, SHAM

Waki’a mai daci ta Karbala, waki’a ce da a tarihin musulunci take da wani matsayi na musamman. Waki’a ce za a iya cewa ta fara ne a daren sha biyar ga watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira shekarar da Mu’awiya ya mutu. Mu’awiyya wanda ya sabawa yarjejeniyar sulhu da suka yi shi da Imam Hasan (as), sai ya zabi dansa Yazidu a matsayin wanda zai gaje shi a mulki har ya karba masa mubaya’a (daga gurin mutane). More
Mar 17 2024
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabalar Da Ta Wakana Tsakanin Dakta Isam Imad Da Shek Usman Kamis
Muƙabala Ta Farko:
Shek Mustafa Ɗa’i (Alƙalin Zama)
Da sunan Allah mai rahama mai jin ƙai; Muƙabala ta farko wadda za a yi ta wannan ofis ɗin da ake kira da (Gurfatul Haƙ) wato ofis ɗin Shi’a Isna Ashariyya.
Sayyid Rafiƙ Musawi kuma shi ne shugaba mai jagorantar zaman daga ɓangaren Shi’a Isna Ashariyya, sai ya ce:
Jan 23 2024
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Muhawarar Mustabsir Ibrahim Kulibali Tare Da Ɗaya Daga Cikin Malaman Sufaye
Ibrahin Kulibali
Karo a Cikin Karo
Kulibali yana ba da labari game da wani abu da ya faru yana mai faɗin cewa: “Mafi yawan rayuwata na yi ta ne a hannun gwaggota; kuma ta kasance tana tsananin ƙaunata har ta kai ga tana ji da ni fiye da ‘ya’yanta, kuma tana burin ina ma dai a ce in zama babban malamin addini in na girma, a saboda haka ne ma take ta ƙarfafani a kan hakan, to kuma dama gwaggon tawa Basufiya ce ‘yar Ɗariƙar Tijjaniya.
Kafar Yadawa
Mar 19 2024
Saƙo Daga Sayyid Basil Khadra’ – Mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu
Saƙo daga mustabsir ɗan ƙasar Falasɗinu samahatul Sayyid Basil Khadra’, a yayin wani shiri na soshiyal midiya (social media).
Ga saƙon nasa kamar haka:
An ruwaito daga Manzon Allah (s.a.w) ya ce: Misalin Ahlilbait ɗina a cikinku kamar kwatankwacin jirgin Nuhu ne, duk wanda ya hau jirgin ya tsira wanda kuma ya ƙi hawa to ya halaka zuwa wuta. Kuma lallai (Annabi) Nuhu (a.s) ya ce wa ɗansa: Ya ɗan ɗana! Zo ka hau tare da mu mana, kada fa ka kasance tare da kafirai!
Labaran Masu Istibsari
Sep 16 2024
Denot Gaetani Lovatelli Ya Zama Shi’a
Denot Gaetani Lovatelli ya fito daga cikin babban gida a Italiya, an haife shi a shekarar 1955, a matsayinsa na mai ɗaukar hoto (camera man) a gidan tv na ƙasa, Luca ya yi tafiye-tafiye zuwa Bosnia da kuma Yammacin Asiya.
Bayan nan ya samu yin tafiya zuwa Afganistan, shi da wani abokin ƙuruciyarsa Edoardo Agnelli, domin aikin tattara bayanai na tarihin ƙasar Afganistan ɗin, wato (documentary).
Sep 16 2024
Ya Karɓi Musulunci A Lokacin Tunawa Da Shahadar Sayyida Zahara (S)
Musulunta A Lokacin Tunawa Da Shahadar Sayyida Zahara (S)
Ɗahir Wardi Shabiriyan ɗan Husain-ƙuli mutumin garin Mahdi-shahar ya Musulunta a majalisin da ake tunawa da zagayowar ranar shahadar Sayyida Zahara (s); saboda irin yadda ya tasirantu da (yadda ake gudanar da majalisin) a nan take ya karɓi kalmar Shahada, kuma ya yi watsi da duk wasu al’adu na jahiliyar tsirface-tsirface marasa tushe tare da mummunar aƙidarsu ta Baha’iyya, sai ya rungumi addinin Musulunci.
Ɗahir Shabiriyan dangane da aƙidun firƙar Baha’iyya yana cewa: A i’itiƙadinsu babu imani da
Sep 15 2024
Na Yi Izgilanci Ga Husain (a.s); Sai Kuwa Allah Ya Kafe Ni Tsugune Waje Guda
Na Yi Izgilanci Ga Husain; Sai Allah Ya Kafe Ni Tsugune Waje Guda
Wasiƙar ɗaya daga cikin ‘yan uwan da suka yi Istibsari:
Assalamu alaikum wa rahmatullah wa barakatuh. ‘Yan uwana ina son in ba ku wani labari game da ni kaina da kuma yadda Allah ya yi mani uƙuba yayin da na yi wa Imam Husain (a.s) izgilanci… Na kasance riƙaƙƙen Bawahabiye. Ba na son Shi’a ko kaɗan, ina ma kafirta su ne kai tsaye, sam-sam ba na masu fatan alheri, kullum ina yi masu tahadidi, sannan ina zaginsu, ina ci masu mutunci… Ana nan sai kawai wata rana cikin ranakun Ashura, ina zaune a gaban talabijin ina kallon tashar ‘yan Shi’a suna ta kuka suna dukan ƙirjinsu domin juyayi (na kisan gillar) da aka yi wa jikan Manzon Allah (s)…
Jul 7 2024
Zainab Kalandari Hurmuzgan ta Shi’ance
Zainab Kalandari Hurmuzgan ta Shi’ance
Sunana Zainab Kalandari mutuniyar garin Hurmuzgan
A wane irin gida kika fito?
Gidanmu gida ne na Ahalissunna kuma a nan aka haife ni.
Mene ne aikinki?
Jun 22 2024
Addinin Musulunci, A Matsayinsa Na Addini Cikakke… Salim Sa’id Al’rajahi

Addinin Musulunci, A Matsayinsa Na Addini Cikakke; Ya Umarci Dukkanin Mutane Da Su Nemi Sani Kuma Su Yi Bincike
Malam Salim Sa’id Al’rajahi ya ce: “Addinin Musulunci, a matsayinsa na addini cikakke; ya umarci dukkanin mutane a kan su nemi sani kuma su yi bincike.
Ya ƙara da cewa: Duk wani wanda yake son ya ɗauki matakin da yake daidai, to lallai ne ya
Jun 11 2024
Taƙaitacce Tarihin Malam Junaid Bello Ibrahim Sakkwato

Taƙaitacce Tarihin Malam Junaid Sakkwato
Cikakken suna: Junaidu Bello Ibrahim, ni haifaffen garin Sakkwato ne, amma asalin kakanninmu Nufawa ne da suka taso daga garin Bidda da ke jihar Neja.
An haife ni a 21 ga watan Agusta 1977 a birnin Sakkwato ta Arewa. A nan Sakkwaton na yi karatun makarantar allo har zuwa na yi saukar Al-Ƙur’ani, kamar dai yadda yake a al’adar kasar Hausa Fulani. Sannan kuma na yi karatun firimare (primary) a Salihu Anka Model School, daga nan sai
May 27 2024
Matashiyar Ba’amerikiya: Babban Dalilin Ɗanfaruwata Da Ahalulbait (a.s) Shi Ne Muhadarorin Addini Da Na Sha Saurare Game Da Masifofin Da Suka Fuskanta…
Matashiyar Ba’amerikiya: Babban Dalilin Ɗanfaruwata Da Ahalulbait (a.s) Shi Ne Muhadarorin Addini Da Na Sha Saurare Game Da Masifofin Da Suka Fuskanta…
Mustabsirar Ba-amerikiya Yasmin Husaj ta ce lallai ta ɗamfaru da Ahalulbait (a.s) ne ta hanyar ƙissoshin da ta dinga saurara a wuraren muhadarorin addini.
May 24 2024
Ƙissar Istibsarin Lauyan Jordan (Attorney) Ahmad Husain Ya’aƙub
Ƙissar Istibsarin Lauyan Jordan (Attorney) Ahmad Husain Ya’aƙub
Mujallar Mimbar a fitowarta ta ranar 10 ga watan zulhijja 1421 Hijiriyya, ta wallafa bayanin Ahmad Husain Ya’aƙub a inda yake sanar da yadda ya yi istibsari da kuma karkatarsa zuwa ga Mazahabar Ahalilbaiti (a.s), saƙon Mujallar ya zo kamar haka:
May 22 2024
Yaya Aka Yi Kika Ƙuduri Aniyar Canja Mazahaba? Lallai Ina Ga Labarin Nan Zai Yi Daɗin Ji
Yaya Aka Yi Kika Ƙuduri Aniyar Canja Mazahaba? Lallai Ina Ga Labarin Nan Zai Yi Daɗin Ji
Wannan labari, labari ne mai tsawo sai dai zan faɗe shi a taƙaice, haka ne ni a da ‘yar Ahalissunna ce kuma ‘yar ɗariƙa. Sai dai ƙwaƙwalwata cike take da tambayoyi. Ina son in san mene ne bambanci tsakanin Sunna da Shi’a. To kuma a saboda haka ne wata rana sai na tafi Zariya, garin da Shek Zakzaki yake rayuwa, a can na ci karo da wasu mata uku sanye da baƙin hijabi, abin sai ya ƙayatar da ni, don kafin wannan lokacin ban taɓa ganin mace da kammalalliyar shiga irin haka ba. Shin me wannan yake nufi, kuma mece ce ma’anar mace ta rufe ilahirin jikinta tun daga sama har ƙasa da baƙin hijabi? Na tambayi goggota. Sai ta ce: Mai ya sa kike tambaya? Ki fita harkarsu ba ruwanki da su! Amma ni wannan maganar ta goggota sai ta sa na ƙara nacewa a kan sai na san dalili.
May 19 2024
Farfesan Jamus wanda ya zama Shi’a

Mashahurin Farfesan Jamus ‘Roderick Agurman’ Ya Shi’ance
Kasantuwar yana son Musulunta, sau uku yana karance Ƙur’ani, Farfesa Roderick Agurman mutum ne mashahuri a nahiyar Turai, mamallakin babban ɗakin gwaje-gwaje na micro Biology a ƙasar Swiss, kuma shi malami ne na tattalin arziki.
Wallafe-wallafen Mustabsirin
Jan 22 2024
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Sunan Littafi: A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Marubuci: Abulmun’im Hasan Sudani
Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jin Ƙai; wannan littafi labari ne mai ratsa zuciya na wani masanin shari’a mutumin Sudan game da yadda ya fahimci mazahabin Ja’afariyya (Shi’a Imamiyya)

Feb 3 2024
LITTAFIN: ALBID’ATU WAL IBTIDA’U
ALBID’ATU WAL IBTIDA’U; Ta’alifin Abdulhamid Al-Jaf.
Silsilatul Kitabi Wassunnati (Halƙa Ta Uku).
Halƙa Ta Uku
Wannan Littafi A Halƙarsa Ta Uku Ya Ƙunshi: Sujjada A Kan Turba Da Bayyana Bisimillah (A Cikin Salla) Da Haɗa Salloli Da Shafa a Kan Ƙafa Da Ɗora Hannu A Kafaɗa Da Sakin Hannu Da Taƙiyya Da Mutu’a.
Dukkan waɗannan bahasosin an yi su a cikin wannan littafin tare da kawo hujjoji da dalilai daga Alƙur’ani da Sunna Sharifiyya.
Littafin an rubuta shi da harshen Larabci, muna ƙoƙarin tarjama shi zuwa harshen Hausa ba da jimawa ba insha Allah.
Mar 13 2024
Hankali a Rayuwar Dan’adam / Dr. Ammar Al-Makki
A cikin wannan shiri mutum zai karu da bayani game da wasu ka’idodi na bahasin Hankali. Shi ko hankali kamar yadda muka sani a gaskiyar magana shi ne mutum saboda ba a komai da marar hankali a rayuwar nan, kai ba a ma lissafa marar shi a matsayin mutum. To kuma a lokaci guda ma’abocin hankalin shi ma yana bukatar ya saita hankalin nasa bisa ka’idodi….Wanda a nan za a ji wasu daga ciki.
Mar 14 2024
ZAGIN SAHABBAI BA MUSULUNCI BA NE1 / MALAM BELLO DANKOLI
Har kullum bayanan da Shi’a suke yi shi ne: Tabbas ba sa zagin sahabbai, domin zagi a Musulunci haramun ne, aya ta fada mana cewa: Kada ku zagi wadanda suke kiran wanin Allah…. Wato Mushirikai da kafirai. To idan zagin su Allah ya hana, ina ga zagin Musulmai kuma Musulman ma sahabbai wadanda suka taimaki Annabi wajen isar da wannan sako na Musulunci.
To amma inda gizon ke saka shi ne: Shi’a suna karanta abubuwan da suka faru a zamanin sahabbai na rigingimu da sakin hanyar da wasu suka yi da kin bin umarnin Annabi na wasici da ya yi masu a Gadir Khum da dai sauran matsaloli. Sai dai mu sani ba fa wai dukkan sahabbai ne suka aikata ba a’a tarihi bai bar mu a duhu ba, ya zayyano mana wadanda suka yi din. Mutum ya je ya bincika zai gani. Fadin hakan kuma ba zagi ba ne sam.
Tarihin Rayuwar Mustabsirin
Sep 16 2024
Taƙaitaccen Tarihin Mustabsir Shek Abdulhamid Jaff
Taƙaitaccen Tarihin Shek Abdulhamid Jaff Daga Muƙaddimar Littafinsa Mai Suna: ‘Summa Shayya’ani Al-Albani’
Shek Abdulhamid Jaff
An haifi ɗan uwa mai girma shek Abdulhamid Jaff, ɗan ƙabilar Kurdawa, a ranar 27 ga watan Ramadan mai albarka a shekara ta 1389h, a gidan Shafi’awa (mabiya mazahabar Shafi’iyya), to amma sai ya tashi daga wannan mazahabar ta gidansu tsaf ya canja zuwa bin Salafanci (ya zama Basalafe), to kuma bayan nan a wajajen ƙarshen shekarar 1993m sai ya sake canja sheƙa zuwa bin mazahabar Ahlulbaiti (a.s) wato Shi’a Imamiyya. Wannan kuma duk ya biyo bayan nazari mai zurfi da bincike da karance-karance dangane da mazahabobin Musulunci da kuma gwama koyarwarsu tare da tantance wacce mazahabar ce ta fi wata tsayuwa a kan dalilai da hujjoji.
Sep 12 2024
Lukman Da Ya Zama Shi’a Nigeria
Luca Gaetani Lovatelli ya fito daga cikin babban gida a Italiya, an haife shi a shekarar 1955, a matsayinsa na mai ɗaukar hoto (camera man) a gidan tv na ƙasa, Luca ya yi tafiye-tafiye zuwa Bosnia da kuma Yammacin Asiya.
Jun 18 2024
Mu San: Shibuli Sharif Ibrahim a Takaice
Takaitaccen Tarihin Sayyid Sharif
Shibuli Sharif Ibrahim
🧿 Haihuwa: An haife shi a unguwar Warure da ke cikin birnin Kano.
🧿 Fadi-tashi na ilimi: Ya yi karatun Alkurani a gidansu a gaban baffansa Sidi Yaro da malam Musa Aminu da malam Awwalu, sannan ya tafi tsangayar malam Tijjani.
Jun 4 2024
Daga Ɗariƙar Ƙadiriyya Zuwa Shi’anci
Daga Ɗariƙar Ƙadiriyya Zuwa Shi’anci
Ganawa da tattaunawa ta ƙud da ƙud da mustabsiri ahalin gundumar Kurdistan ɗin Iraƙi, malam Isa Barzanji, kuma ya ba da labarin yadda ya yi istibsari abin gwanin ban sha’awa kamar haka:
Tarihin Rayuwa:
Ni hadimin Abu Abdillah (a.s) ne a jahar Sulaimaniyya babban birnin al’adun gundumar Kurdistan ta Iraƙi, kuma shugaban al’amuran addinin Musulunci da alaƙoƙi a Husainiyyar Imam Hakim a garin Sulaimaniyya. Sai dai abin damuwa wannan shi kaɗai ne ginin Husainiyya a duk faɗin gundumar Kurdistan.
Ni Shi’a ne kuma mustabsir. Amma a da ni ɗan mazahabar shafi’iyya ne a bisa tafarkin ɗariƙar Ƙadiriyya, cikin godiyar Allah yanzu kam ni ina a kan mazahabar Isna Ashariyya kuma ɗariƙar Ahalulbait (a.s).
Bugawar Cibiya
Jan 24 2024
Bugawa Da Yaɗa Mujalladi Na Farko Na Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Littafin (Mausu’ar) Mustabsirin
Cikin luɗufi na Ubangiji da inaya ta Ahlul Bait Ma’asumai (a.s) tare da tsayuwar-daka da himmar kwamitin ilimi na Cibiyar Mustabsirin wannan littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin an kammala buga shi da yaɗa shi.

An fara yaɗa mujalladi na farko na littafin (Mau’su’ar) Mustabsirin daidai da ranakun tunawa da Shahadar Sayyida Fatima Azzahra (s).
Jan 22 2024
Littafin: Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)
Littafi Mai Daraja Da Aka Rubuta Game Da (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s))
A kwanakin Idin Gadir mai girma da albarka, Cibiyar Mustabsirin ta himmantu da buga tare da yaɗa littafi mai ɗimbin daraja mai suna: (Aƙidar Tauhidi a Makarantar Ahlulbait (a.s)) wato Aƙidar Tauhidi a bisa koyarwar makaranta ta tunani da fikira ta Ahlulbait (a.s), mawallafin littafin shi ne Dakta Ahmad Rasim Al-Nafis mustabsir kuma mutumin Masar.
Wane ne Ahmad Rasim Al-Nafis
– Sayyid Ahmad Rasim Al-Nafis Ma’abocin Himma a Musulunci (Islamic Activist).
– Dan Shi’a Imamiyya.
Dakin Karatu
Sep 16 2024
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Sunan Littafi: A Albarkacin Hasken (Sayyida) Fatima Na Shiriya
Marubuci: Abulmun’im Hasan Sudani
Jul 15 2024
SAYYIDA ZAINAB A FILIN KARBALA FILIN KISAN GILLA😭
BANGARE NA BIYU NA BAYANIN
DAGA MADINA ZUWA MADINA;
AYARIN MASU KUMAJI NA LABARIN
ABIN DA YA FARU A KARBALA DA
ZAMAN MAKOKIN ASHURA
TAFIYAR AYARIN SHAHIDAI DAGA KARBALA ZUWA KUFA
KAMA HANYA DAGA KARBALA
MAI RUWAYA: Bayan wannan waki’a ta ranar Ashura Umar ibn Sa’ad sai da ya kwana daya zuwa biyu a wannan fili na Karbala, sannan aka dora ‘ya’ya da sauran iyalan shahidai a kan rakuma
Jul 11 2024
DAGA MADINA ZUWA MADINA; AYARIN MASU KUMAJI – 8
KARBALA/ 7 GA MUHARRAM SHEKARA 61 BAYAN HIJIRA
MAI RUWAYA: A wannan ranar wata wasikar ta sake zuwa hannun Umar ibn Sa’ad daga Ibn Ziyad a ciki yana cewa:
IBN ZIYAD: Ka killace ruwan Furat ga Husain da sahabbansa kuma kada ka bari su isa gare shi ballanta har su sha!
MAI RUWAYA: Ba tare da bata lokaci ba, Umar ibn Sa’ad ya aika Amara ibn Hajjaj tare da mayaka dari biyar bakin koramar Furat don haka sai ya zama sun hana ayarin masu neman ‘yanci kusantar ruwan na Furat. Ruwan da hatta tsuntsaye da sauran dabbobin daji suka kasance suna sha!
KARBALA/ 8 GA MUHARRAM SHEKARA 61 BAYAN HIJIRA
Jul 10 2024
Yazid Bai Taba Zama Amirul Muminina Ba – Wallafar Shek Nassir Kenya
Yazid Bai Taba Zama Amirul Muminina Ba
Littafi ne wallafin wani mustabsiri dan kasar Kenya mai suna Abdullahi Nassir
Littafin Yana Magana a Kan:
Jagoranci
Shi’anci
Bidi’a
A asali wani dan karamin littafi ne ko a kira shi da (handout) da shek Abdullahi Nassir Mombasa Kenya wanda aka rubuta shi da harshen Sawahili (Yazid Hakuwa Amirul Muminin), daga baya kuma Dakta Muhammad Raza Dungersi ya fassara shi zuwa harshen Turanci.
Jul 6 2024
DAGA MADINA ZUWA MADINA; AYARIN MASU KUMAJI – 4
WAI MENE NE YA FARU A KARBALA NE? 4
MAKKA/UKU GA SHA’ABAN SHEKARA 60 BAYAN HIJIRA
MAI RUWAYA: Bayan Imam Husain (as) ya samu kamar kwanaki biyar zuwa shida yana tafiya, sai ya isa Makka. Mutane suka yi masa kyakkyawar tarba, suka dinga zuwa ziyara da yi masa sannu da zuwa tawaga-tawaga.
KUFA/RAMADAN SHEKARA 60 BAYAN HIJIRA
Jul 5 2024
DAGA MADINA ZUWA MADINA; AYARIN MASU KUMAJI – 3
FARAWAR QISSAR KARBALA, SHAM

Waki’a mai daci ta Karbala, waki’a ce da a tarihin musulunci take da wani matsayi na musamman. Waki’a ce za a iya cewa ta fara ne a daren sha biyar ga watan Rajab shekara ta 60 bayan hijira shekarar da Mu’awiya ya mutu. Mu’awiyya wanda ya sabawa yarjejeniyar sulhu da suka yi shi da Imam Hasan (as), sai ya zabi dansa Yazidu a matsayin wanda zai gaje shi a mulki har ya karba masa mubaya’a (daga gurin mutane). More
Mar 21 2024
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi – Ustaz Marwan Kalifat
Cikin godiya ga Allah fitowar wannan littafi ta kammalu:
Fadlul Shi’ati Alal Ummati Fi Hifzil Ƙur’ani Wal-inayati Bihi
(فضل الشيعة على الأمة في حفظ القرآن والعناية به)
Falalar Shi’a a kan (Sauran) Al’umma
Falalar Shi’a a kan Al’umma a wajen kiyaye Ƙur’ani da kulawa da shi da Shakkala shi da yi masa nuƙuɗa-nuƙuɗa da Tafsirinsa.
Wallafar: Ustaz Marwan Kalifat
Wani yanki na muƙaddimar littafin: Wahabiyawa da waɗanda suka tasirantu da koyarwarsu suna aibata Shi’a kuma suna yawan tuhumar su a kan su kawo ingantaccen sanadi na Ƙur’ani. Yana da ban mamaki lamarin tuhumar nan tasu! Domin wanda gidansa ya kasance na gilas ne, ba zai jefi gidajen mutane da dutsi ba, kamar yadda yake a karin-magana. A saboda haka shin su ɗin sun mallaki ingantaccen sanadin, ballantana a yi maganar tawaturinsa ga ƙira’ar Hafs wacce mafi agalabin Musulmai suke karantawa a yau?!
Mar 13 2024
Husain (a.s): Tsakanin Haihuwa da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi da Haisami
Sunan Littafi: Husain (a.s) A Tsakanin Haihuwa Da Shahada Cikin Ruwayar Zahabi Da Haisami.
Sunan Littafi na Asali: (Al-Husain Alaihil Salam Bainal Wiladati Wal Shahadati Fi Ruwayatil Zahabi Wal Haisami).
Mawallafin Littafi: Shek Nazar Aali Sanbul Al-Ƙaɗifi.
A Dunƙule Littafin ya ƙunshi:
Feb 18 2024
Wahada a tsakanin Muwahhidin
Kira zuwa ga Wahada!
Kira ne na Alƙur’ani wanda ayoyi sukutum Allah (swt) ya saukar domin haɗin kai a tsakanin muwahhidin wato masu addinin saukakke daga Allah (swt) wanda ya ƙunshi dukkan abubuwan da ake buƙata na haɗin kai (saboda yadda haɗin kan yake da matuƙar muhimmanci da kuma fa’idar da ke cikin yin hakan).
Feb 5 2024
Littafi: Ayatul Taɗhir
Littafi: Ayatul Taɗhir
Mawallafi: Muhammad Mahadi Asifi
Bugawar: Majma’ul Alami Li Ahlil Bait (a.s)
Sura: Ahzab; Aya ta 33: Bismillahir rahmanir rahim: Innama yuridullahu li yuzhiba ankumur rijsa Ahlal Baiti wa yuɗahhirakum Taɗhira.
Mawallafin littafin ya yi ƙoƙari sosai wajen kawo hujjoji daga Sunna da Shi’a game da fayyace cewa shin wai su wa ake nufi a wannan aya mai girma, haka nan ya kawo lawazim ɗin da ke tattare da ayar kama daga batun Isma da Tsarki da Tsarkaka daga dukkan datti ko saɓo da sauransu da kuma hukunce-hukunce na shari’a da aka iya fitarwa daga ciki.


















Apr 6 2024
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Shiga Cikin Ƙunci Da Tsananin Rayuwa Ya Zama Sanadin Shiriyata
Bayan bincike mai zurfi da nacewa kan yin addu’oi, na tsinci kaina ina mai miƙa wilayata ga Imam Ali (a.s) a matsayinsa na hasken Musulunci, kuma magajin Manzon Musulunci na haƙiƙa, wanda Allah ne da kansa ya zaɓe shi, ya wajabta mana ƙaunarsa da yin biyayya gare shi.
Ni haifaffiyar ƙasar Czech ce (Jamhuriyyar Czech:) a nan aka haife ni kuma a cocin Katolika aka yi bikin raɗa mini suna domin neman tabarruki, duk da cewa iyayena ba wasu masu kula da addini ba ne can sosai ba, amma dai mun yi imani da Allah sai dai ba ma yin bautar sam-sam. Lokacin da na kai shekara 14 a duniya a lokacin ne na rasa mahaifiyata. Ina ‘yar shekara 18 kuma na yi aure, yanzu haka ina da ɗa a auren da na yi. Amma kasantuwar ƙarancin shekaru, zamantakewar wannan aure sam ba ta yi daɗi ba, zaman aure sam babu fahimtar juna a tsakani.
More
By hs • Kundin Tattara Bayanan Mustabsirin (Encyclopedia) 0